1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Croatia ta nemi afuwa dangane da yaƙin Bosnia

April 14, 2010

Shugaban Croatia Ivo Josipovic yace ƙasarsa na buƙatar zaman lumana da makwabciyarta Bosnia.

https://p.dw.com/p/MwSk
Shugaban ƙasar Croatia Ivo JosipovicHoto: AP

Shugaban ƙasar Croatia Ivo Josipovic ya nemi afuwa dangane da rawar da ƙasarsa ta taka a yaƙin Bosnia. A jawabin da ya yiwa majalisar dokokin Bosnia a a birnin Sarajevo, Josipovic yace yana mai matuƙar juyayi tare da bada haƙuri game da wahalhalu da kuma rarrabuwar kawuna da har yanzu ake da ita a Bosnia. Yace ƙasar Croatia a wannan zamanin tana buƙatar zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da makwabciyarta. Neman afuwar da shugaban ya sanar na daga cikin matakai na baya bayan nan da shugabannin Croatia dana Sabiya masu raáyin sauyi suke ɗauka domin ɗinke ɓarakar da aka samu a shekarun 1990 wanɗanda suka biyo bayan rabuwar Yugoslavia. Mutane kusan 100,000 ne aka yi kiyasin sun rasa rayukansu a lokacin da aka kammala yaƙin a shekarar 2005. A wannan shekarar ne dai Croatia ke fatan kammala tattaunawar shigarta ƙungiyar tarayyar Turai wanda take fatan kasancewa a shekarar 2012.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Zainab Mohammed Abubakar