1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar kwalara ta kashe mutane 51 a Nijar

October 28, 2014

A wani ƙiyasi da aka fitar dangane da cutar a Nijar, aƙalla mutane 51 ne suka rasu daga cikin mutane 1.365 da suka kamu da cutar tun daga farkon shekara kawo yanzu.

https://p.dw.com/p/1Dd2u
Thema Epidemie in Guinea-Bissau
Hoto: DW

A cikin watan Satumba da ya gabata aƙalla mutane 38 ne suka rasu sakamakon cutar ta Kwalara a ƙasar ta Nijar, a cewar ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da agaji na OCHA dake wannan Ƙasa, inda ake ganin hauhawar cutar ta kwalara a wannan shekara, na da nasaba ne da ambaliyar ruwan da aka fuskanta a wurare da dama lokacin damina, inda annobar ta shafi jihohi huɗu daga cikin jihohi takwas na ƙasar da suka hada da Yammacin jihar Tahoua, da Kudu maso gabacin jihar Maradi, da gabacin jihar Diffa, da kuma tsakiyar Jihar Zinder, inda kawo yanzu jami'an kiwon lafiya ke ƙoƙarin kawo ƙarshen ta, tare da neman hana ɓullar ta a wasu yankunan. Hukumar agajin ta OCHA a Nijar ta ce musamman ma a jihar Diffa inda aka samu kwarara 'yan gudun hijira aƙalla dubu 105 tun daga shekara ta 2013 da suka gujewa hare-haran Ƙungiyar Boko Haram, kuma suna yankin wasu tsibirrai na tafkin Chadi inda babu wadatar tsaftatattun ruwan sha.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita Abdourahamane Hassane