Cutar zazzabin Lassa ta bulla a kasar Benin
February 2, 2016Talla
Wata sanarwa da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya fitar, ta ce mutun na farko mai dauke da cutar zazzabin na Lassa, an gano shi ne tun a ranar 05 ga watan Janairu a babban asibitin St Martin da ke Papané cikin karamar hukumar Tchaourou da ke a nisan kilomita 350 a arewacin birnin Cotonou. A cewar Dr Bagou Yorou kawo yanzu dai wannan asibitin na Tchaourou da kuma birnin Cotonou ne aka samu masu wannan cuta.
A watan Octoba na shekarar 2014 ma dai a kasar ta Benin an fuskanci wannan cuta ta zazzabin Lassa.