Shugaban Afirka ta Kudu ya sha ihu
December 16, 2022Talla
Masu zanga-zangar da ke ihun "dole Ramaphosa ya tafi", sun tilasta Shugaba Cyril Ramaphosa yin magana da karfi domin a ji abin da yake fada a jawabin nasa. Wakilan jam'iyyar ta ANC daga sassa dabam-dabam na kasar, na yin taro domin zabar sabon shugaba da ma wanda zai tsaya mata takarar shugaban kasa a zabe na gaba da za a gudanar a shekara ta 2024 a kasar. Shi dai Shugaba Ramaphosa na fatan yin tazarce a mastsayin shugaban jam'iyyar ta ANC da ta kwashe shekaru 28 tana shugabanci a Afirka ta Kudu, duk da zubewar da mutumcinsa ya yi sakamakon zargin almundahana da ma farin jinin jam'iyyar da ke raguwa.