Daidaito kan kundin tsarin mulkin a Sudan
August 3, 2019Talla
An cimma wannan yarjejeniya ne bayan da yunkurin hakan ya cutura sau da dama saboda takun saka tsakanin bangarorin biyu kan shugabanci tun bayan hambara da tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir a watan Afirilun 2019. Fararen hula da dama sun mutu a jerin zanga-zangar neman iko da gwamnati.
Ana sa ran shugabannin bangarorin biyu za su kaddamar da bikin sa hannu kan sabuwar yarjejeniya da zai samar da gwamnatin hadakar soji da farar hula, da za su shugabanci kasar na tsawon shekaru kamin sabon zabe.