"Dakar-Nijar": Hanyar jirgi da ke macewa sannu a hankali
Hanyar jirgi ta gargajiya "Dakar-Nijar" ne babban layin da ke hade kasashen Afirka da dama kama daga Senagal har i zuwa Mali. Sai dai tun shekaru gommai da suka wuce aka fara juya mata baya.
Har yanzu tarago na da kyansa
Ana yi wa tashoshin jiragen kasa na layin "Dakar-Nijar" da suka yi suna a shekarun 1990 rikon sakainar kashi. Alhali a baya hanyar jirgin tana da muhimmaci saboda ta bayar da damar yin jigilar mutane da dukiyoyi tsakanin manyan biranen Senegal da Mali. A yanzu haka shugabannin kasashen biyu Macky Sall da Ibrahim Boubacar Keita sun sha alwashin farfado da wannan hanyar jirgin kasa.
Ciyawa maimakon layin dogo
Babbar tashar jirgin kasa ta Dakar na da tazarar kilomita 1300 a yamma da inda aka shinfida layin dogon. Amma kuma jirage sun daina ya da zango a nan tun da dadewa. An daina sauke mutane a nan tun bayan wani hadarin jirgin kasa da aka yi a shekara ta 2009. Sannan kuma yunkurin da aka yi na rikidar da babbar tashar i zuwa wurin adana kayan tarihi ya ci tura.
Karancin gurabe da yawan turbaya
Jirgi da ake yi wa lakabi da "Petit train da Banlieu" na takaitacciyar tafiya na kilomita 60 daga Dakar zuwa Thiès a kowace rana. Sai washe gari da safe ne yake komawa inda ya taso. Wannan tafiya dai ana yin ta ne tamkar ta hawainiya saboda jirgin ba ya gudu, sannan kuma ana yinta ne cikin kura. Saboda haka ne fasinjoji da dama ke toshe bakinsu a wani mataki na kare kansu.
Kayes na alfahari da jirgi
Bayan iyaka tsakanin Senegal da Mali ne garin Kayes yake. A baya dai rayuwa a wannan gari ta dogara a kan jirgi. Alkaluma sun nunar da cewa a wancan zamani, kashi daya bisa biyu na 'ya'yan wannan gari na aiki ne a kamfanin jirgin kasa. Amma a yanzu mazauna garin na bin motocin fasinja idan suna so su yi balaguro mai tsawon kilomita 500 zuwa babban birnn kasar.
Kyakkyawan tsarin jirgi
Sau biyu ne kadai a cikin mako jirgin ke jigilar fasinjoji daga Kayes zuwa Bamako. Awowi 15 ake shafewa a hanya, kamar yadda jadawali ya tanada. Sai dai a wasu lokutan jirgin na latti ko kuma ya bace a hanya. Lalacewar hanyar jirgin dai ta fara ne tun shekaru da suka gabata.
Komai ya lalace
Bisa matsin lambar Bankin Duniya, gwamnatotin Senegal da Mali sun sayar da hannayen jarin kanfanin jirgin kasa. Tun daga lokacin i zuwa yanzu, kanfanin na ta canja iyayen giji ma'ana wadanda suka sayeshi. Halin da layin dogon ke ciki sai dai addu'a saboda ya dada lalacewa. Ma'aikatan kanfanin sun nunar da cewa ana bukatar sabbin gadaje da layin dogo cikin gaggawa.
Karancin fasinjoji masu kirki
Tsarin sayar da tikiti ba shi da muhimmanci a tashar jirgin kasa na Bamako. Kanfanin jirgin ya yi jigilar sojojin Faransa na rundunar "Serval" daga Senegal zuwa Mali. A farkon shekarun 2000 ma haka lamarin ya kasance, inda aka yi jigilar arzikin karkashin kasa na turawan mulkin mallaka daga Kogin Nijar zuwa gabar ruwan Dakar. Saboda haka ne ma ake wa jirgin lakabi da "Dakar-Nijar".
Jinkiri wajen farfado da kanfanin jirgi
Lokaci zuwa lokaci gwamnatocin Mali da Senegal suna tattaunawa kan gajiyar da za a ci idan aka farfado da hanyar ta jirgi. Idan aka zuba jari, za a iya bunkasa harkokin kasuwanci, yayin da tirelolin da ke jigilar kayayyakin bukatun yau da kullum za su samu taimako. Sai dai har yanzu ba a aiwatar da tsarin ba. Ana rade-radin cewar 'yan China na so su saye hannayen jarin kanfanin na jirgin kasa.