Dakarun gwamnatin Iraƙi sun ƙwace iko da garin Baiji
November 14, 2014Talla
Masu aiko da rahotannin sun ce sake karɓe iko da birni na Baiji da ke a arewacin bagadaza. Zai ƙara ƙwarin gwiwa wa dakarun gwamnatin wajen ƙarfafa tsaro a kan matatar man fetir ɗin da mayaƙan IS suka ƙwace a cikin watan Yunin da ya gabata.
Wannan yunƙurin dai na sojojin gwamnatin na iraki na zaman wata babbar nasara da suka samu a kan masu jihadin tun lokacin da aka fara yin faɗan.