1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Iraki na fuskantar turjiyar Is

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 12, 2015

Kwana guda bayan kutsawarsu birnin Tikrit, dakarun kasar Iraki sun fara fuskantar kalubale daga 'yan kungiyar Is a kokarin kwato mahaifar marigayi Saddam Hussein.

https://p.dw.com/p/1EpGg
Hoto: Reuters/T. Al-Sudani

Sojojin kasar Iraki sun fara jan birki a kokarin da suke yi na mayar da daukacin birnin Tikrit karkashin kulawarsu, sakamakon turjiya da suka fuskanta daga 'yan kungiyar IS. Dakarun na Iraki su yi nasarar kutsawa wannan birni bayan kaddamar da wani gagarumin farmaki tun kwanaki goman da suka gabata. Tun dai watan Junin bara ne masu kaifin kishin Islaman suka kwace Tikrit da ke zama mahaifar marigayi Saddam Hussein daga hannun sojojin gwamnati.

A halin yanzu dai sojojin Iraki sun yi nasarar kwace unguwar Qadisiya da ke a arewacin birnin na Tikrit. Sai dai kuma sansanin sojoji na ci gaba da kasancewa a hannun masu fafutukar kafa daukar Musulunci.

Rahotannin sun nunar da cewa sojojin na Iraki na cin karo da masu harbin sari ka noke da ke boye a kan rufin gidaje da kuma sakuna da lunguna na Tikrit.