Dakarun Iraki na samun nasara kan IS
August 24, 2016Talla
Kwamandan dakarun na Iraki da ke samun goyon bayan sojojin Amirka a yankin da suke da IS din, Nejm al-Jabouri ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewa tuni ma sojojinsa suka kwace iko da matatar mai da ke garin. Sai dai al-Jabouri ya nunar da cewa wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da kungiyra ta IS ta kai da motoci ya dakile yunkurin da dakarunsa ke yi na sake kutsawa wasu yankunan garin na Al-Qayyarah da ke da nisan kilomita 60 da kudancin birnin na Mosul.