1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Isra'ila sun kai hari kan Hamas

Zulaiha Abubakar
December 14, 2017

A safiyar wannan Alhamis din ce sojojin Isira'ila suka kai wani mummunan hari kan 'yan kungiyar Hamas a Zirin Gaza. Rahotanni na nuna cigaba da musayar wuta da bangaren Falastinawa.

https://p.dw.com/p/2pN1y
Gazastreifen Begräbnis nach Luftangriff
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/V. Melnikov

Hare haren na yau na zuwa ne daidai lokacin da ake bukin cikar shekaru 30 da kafa kungiyar ta Hamas da ke yankin Falasdinawa.

Sojojin Isira'ilan sun sanar da cewar zasu rufe iyakokin bangarorin biyu saboda dalilai na tsaro, sai dai babu sanarwa dangane da tsawon lokacin rufe kan iyakokin nasu.

Tashe tashen hankula sun biyo bayan ayyana Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, sanarwar da shugaban Amurka Trump ya yi. Inda ya zuwa yanzu mutum 4 suka rasa rayukansu a zirin  Gaza, a wani yamutsi a kan iyakokinsu tare da jikkata wani 'dan isira'ila.