1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun kawance sun sake halaka mayakan Taliban a Afghanistan

June 30, 2006
https://p.dw.com/p/BusC
A farmakin da suke kaiwa mayakan Taliban, dakarun dake karkashin jagorancin Amirka a Afghanistan sun sake halaka ´yan tawaye 14 da ake zargin cewa masu kishin Islama ne. Rundunar sojin Amirka ta sanar da cewa an gano ´yan tawayen ne dauke da manyan makamai a lardin Nuristan dake gabashin Afghanistan. A wata musayar wuta da aka yi a lardin Kandahar dake kudancin kasar kuma an kashe wani dan tawaye daya. A makonnin da suka wuce dakarun da Amirka kewa jagoranci suka fara kai farmaki akan sansanonin ´yan tawaye Taliban dake kudanci da kuma gabashin Afghanistan.