Dakarun kiyaye zaman lafiya sun mutu a Sudan ta kudu
April 9, 2013Talla
An hallaka sojojin kiyayen zaman lafiya na MDD a Sudan ta kudu. rahotanni suka ce wasu mahara da ba a kai ga tantancewa ba, suka yi wa sojojin da ma'aikata farar hula na MDD kwantar ɓauna. Rundunnar kiyaye zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta kudu wato a taƙaice UNMISS, ta tabbatar da harin, inda ta ce an kuma jikkaa wasu ojoji dama fararen hula, yayin kwantan ɓaunan da ya faru. Sai dai ba a ambaci asalin ƙasashen sojojin da aka hallaka da ke cikin rundunar kiyaye zaman lafiya a Sudan ta kudu.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi