1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Nijar da na Chadi na ci gaba da yakar Boko Haram

Salissou BoukariMarch 9, 2015

Hadin gwiwar dakarun kasar Chadi da na Nijar da suka ayyana wani samame kan 'yan kungiyar Boko Haram, na ci gaba da fatattakarsu don kwato garuruwan da suka kame.

https://p.dw.com/p/1EnTI
Hoto: Reuters/E. Braun

Hakan kuma na zuwa ne bayan da Shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau, ya yi mubaya'a ga kungiyar IS da ke fuskantar tsangwama daga kasashen yamma da ma wasu kasashen Larabawa. A wannan samame dai dubunnan sojoji ne na Nijar da na kasar ta Chadi, da a da suke tsaye tun kimanin wata guda a iyakokin Nijar din da Najeriya kusa da tafkin Chadi, suka soma wannan aiki dauke da tankokin yaki da manyan makammai. Hakan zai basu damar yakar 'yan kungiyar ta Boko Haram a duk inda suka shiga a kasar ta Najeriya, yayin daga nasu bangare dakarun sojan na Najeriya ke nasu samamen.