Dakarun sojojin Iraki sun kwato birnin Fallujah
June 26, 2016Firaministan Iraki Haider Al-Abadi ya kai wata ziyara a wannan Lahadin a birnin Fallujah, bayan da rundunar sojojin kasar ta tabbatar da kwato shi ga baki daya daga hannun mayakan kungiyar IS, inda ya kira al'ummar kasar da su nuna jin dadinsu ga wannan babbar nasara da aka samu ya na mai cewa:
"A yau dakarunmu sun kwato birnin Fallujah, sannan kuma a daidai wannan lokaci dakarun namu na can suna fafatawa a birnin Mossoul. Don haka babu wata malaba ga 'yan kungiyar IS a nan Iraki, zamu kore su daga duk inda suke kamar yadda muka yi alkawarin sake dawo da tutar kasar Iraki a nan birnin Fallujah."
Firaminista Al-Abadi na Iraki ya kara da cewa, nan ba da jimawa ba kuma za su kafa tutar kasar a birnin Mossoul da ke a matsin birni na biyu a kasar ta iraki wanda shi ma yake hannun mayakan na IS. Birnin Fallujah ne dai birni na farko da ya fada hannun 'yan kungiyar tun a watan Janairu na 2014.