SiyasaTurai
Turai na dakatar da ba da mafaka wa 'yan Siriya
December 11, 2024Talla
A baya dai kasashen Sweden, da Norway da Denmark sun sanar da cewa za su dakatar da aikin samar da mafakar. A Jamus ofishin kula da ƙaura da kuma 'yan gudun hijira ya dakatar da duk wasu shawarwari kan neman mafaka daga 'yan kasar ta Siriya. A daren Lahadi ne 'yan tawaye karkashin kungiyar masu kishin Islama Haiat Tahrir al-Sham (HTS) suka mamaye birnin Damascus na kasar Syria, inda suka kawo karshen mulkin Bashar al-Assad.