Iran: Dakatar da dokar wajabta saka hijabi
December 19, 2024Tun a bara ne dai majalisar dokoki a Iran din ta amince da batun na hijabi ga mata, amma sabuwar gwamnatin da ke jan al'amuran kasar ta ce da sauran gyara. Cikin watan Satumbar bara ne kudurin dokar wajabta wa mata sanya hijabin a fadin kasar Iran ya tsallake karatuttukan da aka yi masa a majalisar dokoki aka kuma amince da shi, inda da ma ya rage shugaban kasar ne kawai ya rattaba hannu domin ta kai ga tabbatuwa a fadin kasar. Wannan batu ya kasance wa gwamnatin Iran ta yanzu wadda ke shan suka a ciki da ma wajenta wani karfen-kafa, inda shugaban kasar mai ra'ayin kawo sauyi Masoud Pezeshkian ya dakatar da ita tare nuna cewa tana iya haddasa tashin tashin-tashina shigen wadda aka gani a 2022 bayan mutuwar Mahsa Amini a hannun 'yansanda masu tabbatar da da'a saboda kin sanya hijabin da ta yi.
A ranar Talatar da ta gabata ma dai mataimakin shugaban kasar Iran Shahram Dabiri ya ce, shugabannin siyasa da na tsaron kasar za su yi wa dokar kwaskwarima. Mataimakin shugaban kasar ya ce su ne suka bukaci majalisar dokoki ta jingine batun, har zuwa abin da hali zai yi. Wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin Iran din da ake ganin masu tsaurin ra'ayi ne suka amince da kudurin dokar mai sarkakiya, wanda ya tanadi hukunci mai tsanani a kan duk macen da ta ki sanya hijabi a fadin kasar. Da ma dai dokar za ta bai wa hukumomin tsaron damar yin amfanin da na'urorin daukar hotunan bidiyo, wajen gano matan da ke kin sanya hijabin. Matakin gwamnatin ta Pezeshkian ya zo ne yayin da Iran din ke kokarin komawa ga tattaunawa da kasashen yammacin duniya, dangane da takunkuman da aka kakaba mata a kan shirinta na nukiliya.