1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako dalibai 28 a Kaduna

Abdul-raheem Hassan
July 25, 2021

Masu garkuwa da mutane sun saki dalibai 28 cikin dalibai 120 da suka sace a farkon watan Yuli a makarantar kwana da ke arewacin garin Damishi a jihar Kaduna, jami'an Cocin sun mika daliban da aka sako ga iyayensu.

https://p.dw.com/p/3y2Hh
Nigeria Kaduna | Entführung Schüler Bethel Baptist School
Hoto: KEHINDE GBENGA/AFP

Rev. Israel Akanji shugaban Baptist Convention, ya ce fiye da sauran yara 80 har yanzu suna hannun masu garkuwa da jama'a, ya zuwa yanzu babu tabbacin lokacin da za a sake sauran yaran da ke tsare.

Sai dai 'yan bindigar sun bukaci kudin fansa har Naira 500,000 (kusan $ 1,200) ga kowane dalibi, amma makarantar ta ce ba ta biya ko sisi ba, sai dai kuma ba ta hana iyayen daliban daukar mataki ba.