Saliyo: Bai wa 'yan mata damar karatu
February 8, 2022A lokacin da matashiya Mariatu Ajiatu Kalokoh ta ke da shekaru 17 a duniya ta fuskanci kalubale na rayuwa, inda sanadiyyar junan biyun da ta samu mahaifinta ya kore ta daga gidansa. Sai dai da jibin goshi makwafta suka sami nasarar shawo kansa, domin ya amince da 'yar tasa ta koma karkashin kulawarshi. Sai dai kuma ta fuskanci tsangwama har a makaranta, inda hatta malamanta kan yi mata zunde tare da kunyata ta a gaban abokan karatunta. Wata rana Mariatu ta na kallon talabijin sai ta gano wata mata 'yar asalin Saliyo Peagie Foday da ke zaune a Sweden da ita ma ta taba fuskantar wannan matsala, kuma hakan ya sanya ta kafa wata gidauniya domin tallafawa 'yan mata da suka fada cikin wannan hali komawa makaranta.
Take kuma, Mariatu ta nemi wannan matar ta dandalin sada zumunta. A shekara ta 2015 bayan barkewar annobar Ebola a kasar ta Saliyo, an sami karuwar laifukan cin zarafin mata da kuma 'yan mata da suka dauki ciki. A dangane da haka ne gwamnati ta dauki matakin hana 'yan matan ci gaba da zuwa makaranta, ko kuma rubuta jarrabawar kammala karatunsu. Sai dai kuma kotun kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta yi watsi da hakan a wancan lokacin, tana mai bayyana matakin a matsayin nuna wariya ga mata. Duk da watsi da su da mahaifin diyar Mariatu ya yi shekaru bakwai da suka gabata, hakan bai sanyaya mata gwiwa wajen ganin ta cimma burinta da ta sanya a gaba ba. Mariatu dai na ganin babu wani abu da zai iya kawo tarnaki ga cikar burin matasa.