COVID-19: Da sauran tafiya a Afirka
April 28, 2020Alkalumma a hukumance da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayar, sun nuna cewa a Tarayyar Najeriya ga misali, mutum 1000 ne za su samu kasa da gado guda daya a asibitocin kwantar da marasa lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa a kasar. A kasar Kenya gadajen sun kai sama da gado daya ga mutum 1000. A jimilce a kasashe 43 na nahiyar Afirka, gadajen kwantar da marasa lafiya na gaggawa ba su kai 5000 ba. Wato gado biyar ke nan ga mutum miliyan daya, yayin da a Turai ake da gadaje 4000 ga mutum miliyan daya a cewar WHO.
Nakasu a tsarin kiwon lafiya
Wadannan alkaluman masu tayar da hankali ne musamman a wannan lokaci da cutar Corona ko COVID-19 ke yaduwa a Afirka. Sai dai babu tabbas ko haka lamarin yake a yanzu, domin a Najeriya alkaluman na tun 2005 ne sannan a Kenya na shekarar 2010 ne.
Da dama tsarin kiwon lafiyar a Afirka ba shi da inganci, kamar yadda Kathryn Tätzsch ta kungiyar tallafawa kananan yara ta World Vision a birnin Nairobi ta bayyana. A birnin Kano da ke arewacin Najeriya ma dai haka lamarin yake. Wakilin DW a jihar Nasir Salisu Zango ya ruwaito wasu masana na cewa gwamnatin jihar ba ta shirya sosai ba wajen tunkarar annobar, inda ma masanan ke saka ayar tambaya a kan alkaluman da gwamnatin ta bayar na yawan adadin masu dauke da cutar.
Tun ba yau ba, hukumar ta WHO ke gargadin cewa Afirka ka iya zama zango na gaba da annobar Corona za ta yi kakagida. A hasashenta, cutar ka iya hallaka mutane dubu 300 a Afirka, sannan fiye da miliyan 30 za su iya shiga matsanancin hali na talauci.
Wata matsalar ma ita ce karancin na'urorin gwaje-gwaje na cutar. Masu binciken kimiyya a Makarantar nazarin magungunan yankuna masu zafi da ke birnin London na kasar Birtaniya, sun ce al'akaluman da ake bayarwa a Afirka na da nakasu.
Gwamnatoci ba su shirya ba
Francesco Checci mai binciken kimiyya ne a makarantar: "Alkaluman da ake bayarwa dangane da yaduwar cutar da yadda tsare-tsaren kiwon lafiya suka shirya tinkarar cutar ba masu gamsarwa ba ne. Damuwarmu dangane da yaduwar cutar shi ne, matsalolin da ke tattare da yadda aikin gwaje-gwaje ke gudana a mafi yawa na kasashen Afirka. Wato abin nufi ba za a iya yarda da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a nahiyar ba."
Masanin ya ce ba wanda ya san iya shirin da Afirka ta yi na tinkarar annobar. Abin da ya rage kawai shi ne mayar da hankali wajen daukar sahihan matakan rigakafi, wanda da ma masu iya magana kan ce ya fi magani.