A Yuganda dan adawa zai koma gida daga jinya
September 19, 2018Talla
A wannan Alhamis aka tsara mawakin da ya rikide ya zama dan majalisar dokokin kasar Yuganda a bangaren adawa Bobi Wine zai koma gida bayan jinya a kasar Amirka sakamakon gallazawa da ya fuskanta daga hukumomin tsaro.
Shi dai Bobi Wine wanda asalin sunansa shi ne Kyagulanyi Ssentamu an zarge shi da taka rawa lokacin da ake jefar tawagar Shugaba Yoweri Museveni lokacin yakin neman zaben cike gurbi na majalisar dokoki. Yanzu haka Ssentamu belinsa aka bayar kuma lauyansa ya ce tuhumar da ake wa dan siyasan na cin amanar kasa babu wasu shaidu.
Kyagulanyi Ssentamu ya ce yana gwagwarmaya da Shugaba Yoweri Museveni ne domin tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki a kasar ta Yuganda.