Salah Khashoggi yabar Saudiyya
October 25, 2018Talla
A karon farko Saudiyya ta amince da hujjojin Turkiyya na cewa an dade da shirya kisan fitaccen dan jaridar da ke rubuta wa jaridar Washington Post. Kamfanin dillancin labaru na Saudiyya ya ruwaito babban mai shigar da kara na Saudiyya bin Abdalla na cewa wadanda suka kashe dan jarida Jamal sun aikata kisan da gangan, duk da cewa Saudiyyan ta yi ta fitar da bayanai masu karo da juna kan kisan.
Saudiyya na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga manyan kasashen duniya kan bayyana hakikanin gaskiyar abinda ya faru da dan jaridar bayan da aka gayyace shi zuwa ofishin jakadancinta da ke Turkiyya ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2018.
Shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana kisan a matsayin rufa-rufa mafi muni a tarihi.