1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan kasar Faransa cikin 'yan IS

November 17, 2014

Faransa ta ce akwai kwakkwaran zaton cewa wanda aka nuna a sabon faifayen vedio 'yan kungiyar ta'addan IS dan kasarta ne.

https://p.dw.com/p/1Dogn
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ministan harkokin cikin gida na kasar Faransan Bernard Cazeneuve ne ya bayyana hakan, inda ya ce mutumin da aka nuna sanye da bakaken kaya kuma dauke da kan mutum da ya bayyana da jam'in agajin kasar Amirka dan kasar Faransa ne. Cazeneuve ya ce tuni jam'ian tsaron kasar Faransan sun yi nazarin faifen Vedio, inda suke kyautata zaton dan kasar ne. A wannan Lahadin ne dai 'yan ta'addan na IS suka saki faifen Vedio wanda ya nuna mutumin dauke da kai ga kuma gangar jiki jikin jini kwance a gabansa tare da bayyana mutumin da jami'in bada agaji dan kasar Amirka da suka sace a watan Oktobar shekarar da ta gabata ta 2013 a Siriya Abdul-Rahman allias Peter Kassig

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman