Dan shugabar Laberiya ya sha kaye a zaben kasar
December 23, 2014Dan gidan shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta Laberiya Robert Sirleaf ya sha kaye a hannun shahararran tshohon dan wasan kwallon kafar kasar George Weah a zaben majalisar dattawan kasar da ya gudana a karshen makon da ya gabata.
Gidan rediyon Veritas a kasar ta Laberiya ya bada wannan rahoto.
Takarar dai ta George Weah da Robert Sirleaf ta zama takara mafi zafi da ta dauki hankulan al'umma a zaben kasar ta Laberiya wanda aka dage har sau biyu tun daga watan Oktoba saboda fargabar cutar Ebola.
Weah da ya zama dan wasan da yafi kowa bajinta a duniya kamar yadda Hukumar FIFA ta bayyana a shekarar 1995, shi ya kafa jam'iyyar Congress for Democratic Change da ke adawa ya kuma samu kashi 80 cikin dari na kuri'un da aka kada a yankin Montserrado kamar yadda sakamakon zaben na yammacin jiya Litinin ya nunar.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu