1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan mutane sun hallaka a Mosul

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 25, 2017

Wani harin jiragen yakin rundunar da Amirka ke goyon baya, da aka kai a birnin Mosul na kasar Iraki ya hallaka mutane da dama.

https://p.dw.com/p/2ZxOl
Daruruwan mutane sun hallaka a karkashin gine-gine a Mosul
Daruruwan mutane sun hallaka a karkashin gine-gine a MosulHoto: Reuters/Y. Boudlal

'Yan gudun hijira a wannan yanki sun bayar da bayanan cewa daruruwan mutane ne aka binne a karkashin gine-gine a yayin harin jiragen yakin, a kokarin fatattakar 'yan kungiyar IS a wannan yanki. shima gwamnan gundumar ta Mosul Nawfal Hammadi ya tabbatar da cewa sama da fararen hula 130 ne suka hallaka a 'yan kwanakin nan, a ci gaba da kai farmaki ta sama da jiragen yakin ke yi, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa mutane da dama sun hallaka, kana har kawo yanzu akwai fararen hula sama da 400,000 a yankin na Mosul. Ga guda ne daga cikin 'yan uwan wadanda suka rasa rayukansu yayin harin, inda yake cewa:

"Ya za a yi su kai hari irin wannan da manyan bindogogi an atilare a yankin da fararen hula suke? Kafin fara kokarin kwace iko da yankin yammacin Mosul, sojojin Amirka da na Iraki sun tabbatar mana da cewa za su saukaka yakin ta yadda ba zai shafi fararen hula ba, shi yasa mutane basu kaurace wa gidajensu ba. Wannan ba kokarin kwace garin ba ne, kawai ruguza garin suke yi."