1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Hathloul: Hukuncin shekaru biyar a gidan yari

Abdoulaye Mamane Amadou
December 28, 2020

An yanke hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ga matashiyar nan 'yar fafutika da ta jima tana da'awar ba wa mata 'yancin tukin mota a Saudiyya.

https://p.dw.com/p/3nI8f
Saudi-arabische Aktivistin Ludschain al-Hathlul
Hoto: Marieke Wijntjes/Amnesty International/dpa/picture alliance

Wata kotu a Saudiyya ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ga matashiyar, bisa tuhumarta da aikata laifin tada zaune tsaye. 'Yar shekaru 31 a duniya da kuma ta sha fafutikar ganin an bai wa mata 'yancin tuka mota a Saudiyya, Loujain al-Hathloul daman ta shafe tsawon shekaru biyu a hannun hukuma a gabanin hukuncin kotun. Sai dai tuni bangarori daban-daban na duniya suka fara sukar matakin kotun irinsu Jadakadan Iceland a Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya ce 'yan fafutikar kare hakin dan Adam da kungiyoyin fararen hula ya kamata su taka muhimiyar rawa wajen sauye-sauyen da Saudiyya ke aiwatarwa yana da kyau a saki duk wadanda aka kama ciki har da Loujain al-Hathloul.