Dokar hana yi wa mata kaciya a Gambiya
December 29, 2015Talla
Wannan sabuwar dokar da aka aminta da ita a Yammacin ranar Litinin, ta tanadi hukunci har na shekaru uku a gidan kaso, da kuma tara ta kwatankwacin dallar Amirka 1.300. A cewar Asusun Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yara kanana UNICEF, kasar Gambiya na daya daga cikin kasashe 10 kuma dukanninsu na Afirka inda aka fi yi wa mata kaciya, wanda hakan ya shafi uku daga cikin hudu na matan kasar.
Ana ganin dai wannan sabuwar doka za ta taimaka wajen samar wa matan kasar 'yancin tare da karesu daga wannan muguwar dabi'a da ke da babbar illa ga lafiyarsu a cewar mataimakiyar shugaban kasar ta Gambiya Isatou Njie Saidy yayin da take magana a gaban 'yan majalisun dokokin kasar da suka kada kuri'ar da babban rinjaye.