'Yan jarida na cikin kunci a Tanzaniya
August 12, 2020Talla
Masu rajin kare hakkin 'yancin 'yan jarida sun yi kira a sake nazarin sabuwar dokar wadda ke neman dakile ayyukan kafofin yada labarai a Tanzaniya.
Tuni dai kafofin yada a Tanzaniya suke yada shirye shirye na wasu kafofin yada labarai na kasashen waje da suke hulda da su.
Sai dai kuma a yanzu da wannan mataki sai gidajen Radiyo da Talabijin din na cikin gida sun nemi amincewar gwamnati sannan kuma su gabatar da yarjejeniyar da suka cimma da kafafen yada labaran na ketare ga hukumar da ke sa ido kan kafofin yada labaran na cikin gida domin amincewa.
Daukar wannan mataki dai ya biyo bayan wata hira ce da wata tashar gidan radio Free Afrika ta yada wadda BBC ta yi da jagoran adawa Tundu Lissu.