Dominique Strauss Khan ɗan takara EU a shugabancin IMF
July 10, 2007Ministocin Kuɗi na ƙasashe 27 membonin ƙungiyar taraya turai, sun cimma daidaito, a game da takara Dominique Strauss Kahn, na ƙasar France ,a matsayin saban shugaban assusun bada lamani na dunia.
A wani ɗan taƙaitacen jawabi, da ya gabatar, DSK ya bayyana gamsuwa da wannan nasara , tare da miƙa godiya ta musamman, ga shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy, da ya ɗora ma sa wannan yauni.
Dominique Strauss Khan ɗan jam ´iyar PS mai adawa,na ɗaya da yan takara da su ka buƙaci shiga takara, shugabancin ƙasar France, amma ya sha kayi, daga abikiyar hammayar sa, Segolene Royal.
Jean Luc Biacabe, wani jami´i a majalisar kasuwanci da masana´antu ta ƙasar France, ya bayyana wajibcin takara Dominique Strauss Kahn.
A watan oktober ne na wannan shekara, shugaban asusun bada lamani na dunia, Rodrigo de Rato na ƙasar Spain, ya yanke wa kansa shawara ajje muƙamin sa, a kan wasu dallilai na ƙashin kan sa ,da bai bayyana ba.