1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya gana da mataimakinsa Mike Pence

Abdoulaye Mamane Amadou
January 12, 2021

Shugaba Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence, sun yi alwashin hada karfi da karfe don ci gaba da mulki tare da tunkarar abokan hamayya na jam'iyyar democrat.

https://p.dw.com/p/3noAw
Donald Trump und Mike Pence
Hoto: picture-alliance/AP/S. Walsh

A yayin ganawar su ta farko a yammacin ranar Litinin tun bayan hargitsin da magoya bayan Donald Trump suka tayar a harabar majalisa dokoki ta Capitol, Mista Trump da Pence, sun soki yadda magoya bayansu suka tayar da fitinar.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da a ranar Laraba ake sa ran majalisar dokokin Amirka za ta yi wani zaman na musamman don duba bukatar da 'yan jam'iyyar democrat suka shigar, na tsige shugaba Trump gabanin kawo karshen wa'adin mulkinsa a ranar 20 ga wannan watan na Janairu.

Jam'iyyar democrat na zargin shugba Trump ne da ingiza magoya bayansa su tada zaune tsaye a majalisar, lamarin da suka kira wata babbar barazana ga tsaron kasar Amirka.