Donald Trump ya shiga halin tsaka mai wuya
December 13, 2017Talla
Nasarar ta Doug Jones wacce ta zo bazata, ita ce nasara ta farko da jam'iyyar Dmocrat ta samu a Jhar Albama a cikin kusan shekaru 25. Roy Moore wanda ke da goyon baya shugaban Amirkan Donald Trump an sha yi masa zarge-zarge na cin zarafi wasu 'yan mata. Da wannan nasarar da jam'iyyar ta Democrat ta samu za ta iya samun rinjaye da kujeru 51 a zaben zauren majalisar dattawan a shekara ta 2018