Dos Santos ba zai tsaya takara ba a 2017
March 11, 2016Shugaban Angola Jose Eduardo dos Santos ya bayyana cewar ba zai sake tsayawa takara ba bayan cika wa'adin mulkinsa a shekara ta 2017. Yayin wani jawabin da aka watsa ta kafar rediyo ne shugaban mai shekaru 73 da haihuwa ya yi wannan shelar da ta zo a bazata. dos Santos wanda ya dare kan kujerar mulkin Angola a shekarar 1979, ya na daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a mulki a nahiyar Afirka.
Jam'iyyar MPLA da ke mulkin Angola za ta shirya babban taro a cikin wannan shekara ta 2016 da nufin zaban sabbin shugabanni tare da daura damarar tinkarar zabuka masun zuwa. Angola dai ita ce kasa ta uku da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, kana ta biyu wajen hako arzikin man fetur baya ga Najeriya.
shgugaba Dos Santos ya ce zai wanke hannayensa daga harkokin na siyasa don mutunta kundin tsarin mulki.
"A shekara ta 2012 ne na yi tazarce a zaben gama gari da aka shirya. Kuma kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanata, wa'adin muki na zai kare ne a shekara ta 2017. Saboda haka ne na yanke shawarar raba gari da siyasa a shekara ta 2018."