Rikicin ya raba dubban mutane da gidajensu
May 9, 2023Majalisar Dinkin Duniya ta ce fada da ake ci gaba da fafatawa a kasar Sudan ya janyo fiye da mutane 700,000 sun tsere daga gidajensu kuma wannan alkaluma ne na mutanen da suke cikin kasar ba su samu damar ficewa ba, inda alkaluman suka nunka cikin mako guda.
Masu aikin agaji suna ci gaba da aikin cikin mawuyaci hali sakamkon yakin tsakanin sojojin gwamnati da kuma rundunar kai dauki ta RSF. Fadan ya kai ga mutuwar daruruwan mutane yayin da wasu dubbai suka jikata.
A tsakiyar watan jiya na Afrilu fada ya barke tsakanin dakarun Sudan karkashin shugaban gwamnnatin wucin gadi Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo wanda yake jagorancin rundunar RSF kuma duk yunkurin tsagaita wuta da kasashen duniya ke yi ya ci tura.