1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban yara na fama da tamowa a Jigawa

Zainab Rabo/USUMarch 2, 2016

An bayyana cewa jihar Jigawa ita ta fi kowace jiha yara da ke fama da cutar tamowa, asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya furta hakan

https://p.dw.com/p/1I5kw
In Afrika hungern immer noch Menschen
Matan Afirka da ke fama da tamowaHoto: AP

Babban jami'in UNICEF a Najeriya Mr. Arjan de Wagt, shi ne ya bayyana hakan a Dutse fadar gwamnatin jihar Jigawa, ya ce kididdigar da hukumar ta gudanar ya nuna cewa, yara da ke kasa da shekaru biyar 600,000 daga cikin 1.100,000 da ke jihar, ke fama da cutar tamowa, cutar da rashin abinci mai gina jiki ke haddasawa.

Jami'in na UNICEF yace yara 160,000 ke fama da tsananin cutar, wadda idan ba a dauki matakin gaggawa ba za a iya samun karuwar 32000. Yace rashin bayar da nono zalla na tsawon lokaci, shi ne ya jawo hakan, domin mata masu ciki 17000, basa samun sinadarinn gina jiki na Vitamin da zai hana su kamuwa da cututtuka, yara dubu dari 650,000 ke fama da rashin sinadarin Vitamin A.
UNICEF Bericht Kind Behinderung Dritte Welt Liberia
Yaran matalauta a kasashe masu tasowaHoto: picture-alliance/AP Images
Dr. Kabiru Ibrahim shi ne darakta a matakin lafiya na farko a jihar Jigawa, ya fadawa DW cewa. "Lamari ne wanda ya wuce ma'aikatar lafiya, ya shafi kowa da kowa. Domin kafin UNICEF ta fitar da alkauman, akwai tsari da muke yi na yaran da suka kamu da cutar ta tamowa. Amma yanzu za mu kara fadada shirin zuwa asibitoci 60 a jihar Jigawa, domin fadakar da mata tare da kawo musu abin da ya kamarta su ci, yayin goyon ciki da kuma tsarin bayar da nono zalla".
Su kuwa matan da yaransu suka kamu da cutar tamowa suna bayyana abinda ya faru da cewa talauci ne. Wadanda suka yi magana da DW, sun nemi a sakaye sunanayensu. "Yunwa ce, domin bama samun abinci, yara duk sun rame in ka ci na yau kana neman na gobe, domin zuwa asibitin ma sai da kyar".
Wannan matar kuwa cewa ta yi. "Ba ruwa, idan yaro yana ja azaba ta isheki, dan ciwo ganye zaka tsinko ka kwadanta shi, shi ma yanzu ya kare. Mu muna so, dabbobi na so. Zogale yanzu ya zama na masu kudi, domin shigowa suke kauye su saye, suna dafawa, ruwansa ana kullawa murtala.