1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara da dama za su mutu a dalilin Corona

Gazali Abdou Tasawa
May 13, 2020

Hukumar Kula da Yara ta MDD wato Unicef ta yi gargadin cewa yaki da annobar Coronavirus na iya dalilin mutuwar kananan yara dubu shida a kowace rana ta Allah a kuma tsawon watanni shida a kasashe matalauta.

https://p.dw.com/p/3c9CB
Afghanistan humanitäre Hilfe
Hoto: picture-alliance/AP/R. Maqbool

Hukumar Kula da Yara ta MDD wato Unicef ta yi gargadin cewa matakan yaki da annobar Coronavirus na iya haddasa mutuwar kananan yara dubu shida a kowace rana ta Allah a kuma tsawon watanni shida a kasashe matalauta.

 Wani bincike da Jami'ar Johns Hopkins ta kasar Amirka ta gudanar ya nunar da cewa idan dai har mafi muni daga cikin wasu jerin hasashen guda uku da binciken ya yi ya tabbata, to kuwa kananan yara miyan daya da dubu 200 'yan kasa da shekaru biyar na iya mutuwa a cikin kasashe 118 a sakamakon yadda matakan yaki da annobar Corona za su hana kula da lafiyar yaran kamar yadda ta kamata, wannan kuwa baya ga dama wasu kananan yaran miliyan biyu da rabi da ke mutuwa a kowadanne watannin shida a wadannan kasashe matalauta.

Kazalika rahoton ya ce mata dubu 56 da 700 na iya halaka sabili da karancin ba su kulawa a lokuttan haihuwa ko bayan haihuwar ta dalilin mayar da hankali ga yaki da Covid 19