Duniya na Allah wadarai da abinda ya faru a Amirka
January 7, 2021Kasashen China da Rasha da Iran da dama ke takun saka da gwamnatin shugaba Donald Trump, a cikin wani yanayin zumde sun yi bayyana abin da ke faruwa a Amirka a matsayin raunin dimukuradiyya.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana kaduwa tare da fatan ganin kasar ta dawo hayyacinta, a yayin Shugaba Emmaneul Macron na Faransa, ya yi kakkausar suka ga matakin na magoya bayan Donald Trump, yana mai cewa " Ba za mu bari wasu kwarorin masu tayar da zaune tsaye su mayar da hannun agogon ci gaban dimukuradiyya baya ba".
Haka suma sauran shuwagabannin a kasashen Isra'ila da Kanada da Austriya da Holand da Spain da Nerland, duk sun yi kakkausar suka kan matakin.
Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeie a wani sakon bidiyiyonsa, ya bayyana kaduwa da abinda ya faru a harabar majalisar dokokin ta Amirka. "Ya ce Bacin rai da kyama na saka dimukuradiyya cikin hadari, haka kuma karya da tashe-tashen hankula na kasancewa babban hadari ga tsarin dimukuradiyya."