Za a rage amfani ta leda a duniya
March 15, 2019Talla
Kasashen sun dauki wannan alkawarin ne a babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan muhalli da aka kammala a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Kasashen sun kuma yi alkawarin daukar matakan magance matsalolin muhalli da suka hada da ledoji da dangoginsu nan da shekarar 2030
Sai dai sanarwar bayan taron ta sassauta bisa bukatar Amirka wadda ta nuna adawa da daukar matakai masu tsauri kan kayayyaki masu gurbata muhalli.
Tun da farko dai an yi fatan cewa kasashen za su haramta amfani da leda baki daya.
A cewar shugaban zauren Majalisar Dinkin Duniya Siim Kiisler yana da matukar wuya a iya samar da matakin bai daya ga dukkan kasashe.