Duniya ta sa ido kan sulhun Sudan ta Kudu
May 5, 2016Babbar jami'ar diflomasiyya da ke wakiltar Sakataren MDD a rikicin Sudan ta Kudu Hallen Margret Loej ta jaddada bukatar bangarorin Kiir da Machar da su gaggauta fara aiwatar da ragowar jadawalin cimma yarjejeniyar zaman lafiyar da suka sanya hannu kansa a birnin Addis Ababa na Habasha.
Ta ce "Yanzu ya rataya a wuyar gwamnatin hadin kan kasa da ta sake matsa kaimi wajen kammala dukkanin wasu rukunonin da ke cikin yarjejeniyar samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu."
Hellen Margret ta kara da cewar Majalisar Dinkin Duniya na matukar muradin ganin an kawo daidaito kan shirin kafa rundunar 'yan sandan kasar na bai daya. A karkashin yarjejeniyar dai an tanadi cewar 'yan sandan Riek Machar za su narke cikin rundunar 'yan sandan kasar.
Sai dai tun da mataimakin shugaban kasar Riek Machar ya shiga ofishinsa hakan bai tabbata ba, inda har yanzu akwai 'yan tashe-tashen hankula a wasu sassa daban-daban na Kasar ta Sudan ta Kudu.
Jami'ar ta kara da cewa "akwai bukatar magance matsalar tallafin da al'ummar kasar suke bukata, gwamnatin hadin kan kasar ka iya tallafawa wajen bayar da damar mika kayayyakin agaji ta hanyar soke shingayen kan tituna."
Wani batu da ke daukar hankalin MDD shi ne na kirkiro da jihohi 28 a Sudan ta Kudu.Sai dai takaddama tsakanin Salva Kiir da Riek Machar ya dabaibaye wannan yunkuri. A watan Nuwamba ne Shugaba Kiir ya keta jihohi goma da kasar take dasu zuwa 28 a inda Machar wanda a wancen lokacin ke zama madugun 'yan tawaye yayi watsi da shirin kirkiro da jihohin.
Sai dai masu fafutuka na kungiyoyin fararen hular Sudan ta Kudun ciki har da Edmond Yakini da ke zama Darektan wata kungiyar kawo ci gaban al'ummomin kaasar. Ya yi kira da a "kammala shirye- shiryen majalisa wajen kafa majalisar dokokin kasa, sannan a samu hukumar zabe mai zaman kanta da dukkanin cibiyoyi a matakan kasa."
Batun tsaro na daya daga cikin muhimman bangarorin da al'ummomin kasa da kasa ke matukar son ganin dukkanin bangarorin biyu na Sudan ta Kudu sun kai ga cimmawa cikin nitsuwa.