DW ta bai wa Sedat Ergin lambar yabo
April 21, 2016
Sedat Ergin na ɗaya daga cikin yan jaridun Turkiyya da ke fuskantar ƙalubale daga gwamnatin sakamakon rubuce-rubuce da jaridarsa take na sukar gwamnatin.Kuma yanzu haka yana fuskantar shari'a sakamakon zargin da ake yi masa da laifin yin ashar ga shugaban ƙasar na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
A karo na biyu ne dai jere magoya bayan jam'iyyar da ke yin mulki watau AKP ke kai wa jaridarsa hari. DW ta ba da wannan lambar yabo ce ga wannan ɗan jaridar domin jinjina masa a fafutukar da yake yi na kare hakin ɗan Adam da yancin faɗar albarkacin bakin 'yan jarida da kuma tabbatar da dimokaraɗiyya.A shekarar bara DW ta ba da irin wannan lambar yabo ce ga wani mai nazari shafin intanet na Blogger ɗan asilin ƙasar Saudyya wanda shi ma ake tsare da shi a gidan kurku.