DW ta karrama masu ba da labarai kan Corona
May 3, 2020Da yake jawabi a Berlin bayan sanar da sunayen wadanda suka samu lambar yabon, babban daraktan kafar yada labarai ta DW Peter Limbourg ya ce lokacin da duniya ke cikin tashin hankali na annoba, a lokacin ne da aikin jarida ke da babban kalubale. Shugaban na DW ya ce yancin 'yan jarida na cikin hadari a fadin duniya domin a cewarsa wasu kasashe na fakewa da annobar Corona wajen yaki da 'yan cin fadin albarkacin baki na 'yan jarida da ma walwalarsu.
Al'ummar ko wace kasa na da 'yan cin samun bayanai masu inganci dangane da halin da ake ciki, ko yaya labarin yake. Toshe hanyoyin samun bayani ko kuma zargin rahotannin da ake yayatawa kan ainihin halin da ake ciki ya sabawa 'yancin fadin albarkacin baki, a cewar Peter Limboug.
A jawabinta albarkacin wannan karramawa da aka yi wa 'yan jaridar a wannan rana, shugabar hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet cewa ta yi ''al'umma da dukkanninmu na bukatar sahihan bayanai dangane da wannan annoba tare da sanyamu cikin dukkan matakan da ake dauka a madadinmu"
Tun bayan bullar Covid 19 dai, kungiyoyin 'yan jarida sun tsinci kansu cikin ukuba saboda rahotannin da suke gabatarwa. Kungiyar kare hakkin jarida ta kasa da kasa ta Reporter Without Borders ta ce gwamnatocin da ke da salon mulkin kama karya a sassa daban-daban na duniya suna amfani da wannan lokaci wajen samun hanyar cin zarafin 'yan jarida saboda basa son a san halin da suke ciki.
Cibiyar 'yan jarida ta kasa da kasa ta tattara bayanai sama da 150 kan yadda ake sabawa dokokin na baiwa 'yan jarida 'yancin tafiyar da ayyukansu, wadanda ke da nasaba da wannan annoba, ta kuma yi misali da Chaina inda cutar Coronavirus ta fara bulla a watan Disambar 2019. Duniya ta ji a jikinta saboda tsarin kasar na bayar da bayanan da take so a ji kawai.