A labarin da ta buga kan cutar ta Ebola jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa Kwango na da babbar kwarewa wajen yaki da Ebola, amma sake bullar cutar a wannan lokaci na zama mafi girma. Jaridar ta ce a ranar daya ga watan Augustan bara lokaci da ma'aikatar kiwon lafiya a Kwango ta tabbatar da cewa kwayoyin cutar Ebola suka sanadin mutuwar mutane 20 a garin Mingina da ke gabashin kasar, ta yaba da wannan binciken da cewa zama shaida yadda tsarin sanya ido kan masu fama da cutar ke aiki. Sai dai shekara guda bayan haka alkalumman da hukuma ta bayar sun nuna cewa mutane fiye da 1800 cutar ta yi ajalinsu a gabashin kasar, duk da samun allurar riga kafi karo na farko, duk kuwa da yadda ake gaggauta matakin yaki da yaduwar kwayoyin cutar. Zaman dardar na karuwa a yankin gabashin kasar musamman tun bayan mutuwar wasu mutane biyu a ranar Laraba a Goma babban birnin lardin.
Shekaru 10 ke nan mayakan yan ta’adda suka addabi yankin Arewa maso Gabashin Najeriya amma har yanzu an kasa maganin rikicin. Wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta buga dangane da cika shekara 10 da fara rikicin Boko Haram a Najeriya. Jaridar ta ce hakan ya zo yayin da har yanzu Boko Haram ke aikata ta’asa inda jaridar ta ba da misali da harin da ‚yan ta’adda suka kai kan masu jana’iza a kusa da birnin Maiduguri inda suka halaka fiye da mutum 60 a karshen mako. Jaridar ta kara da cewa duk da yake hare-haren Boko Haram sun yi sauki idan aka kwatanta da shekarun baya, amma dole gwamnatin Najeriya ta yi da gaske matukar tana son ta ga karshen rikicin. Abin da yanzu za a iya cewa na da wuya domin kasancewa gwamnatin tana fama da rikicin ‚yan Shi’a da ke bukatar gwamnati ta saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ke tsare tun karshen shekarar 2015, duk umarnin da kotu ta bayar da a sake shi domin ya nemi magani a ketare.
A karshe sai kasar Angola mai fama da tabarbarewar tattalin arziki duk da kasancewarta kasar Afirka ta biyu da ta fi arzikin man fetur. A sharhin da ta rubuta jaridar Die Tageszeitung ta ce a tsakiyar matsalar koma-bayan tattalin arzikin gwamnatin za ta gina sabuwar unguwa ta kasaita a Luanda babban birnin kasar. Ko da yake ba a san yawan kudin da aikin zai lakume ba amma ana kara nuna damuwa cewa za a ta da mazauna da ke kusa da unguwar da ke gabar teku, inda fadar shugaban kasa da kuma sabon ginin majalisar dokoki suke. Aikin dai ya kunshi ma’aikatun gwamnati 28 da wasu hukumomi da cibiyar kasuwanci da gine-ginen kasaita da wuraren shakatawa. Tambaya da ake ita ce mai yasa gwamnati z ata yi wannan aiki yayin da al’umar kasar ba su da tsabtataccen ruwan sha, babu hasken wutar lantarki harkokin ilimi sun tabarbare. Jaridar ta ruwaito masana a kasar na cewa kamata ya yi gwamnati ta ba da fifiko wajen yaki da matsalar talauci da ke karuwa tsakanin al’umma maimaikon wannan aiki na kasaita.))