1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: ECOWAS za ta sake zama kan NIjar

August 7, 2023

Kungiyar ECOWAS za ta sake zama a ranar Alhamis mai zuwa, domin neman mafita kan juyin mulkin Nijar bayan cikar wa'adin da ta ba wa sojoji na su koma bariki ko kuma a koresu da karfi tuwo.

https://p.dw.com/p/4UsYf
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

A cikin sanarwar da kungiyar ta fidda a wannan Litinin ta ce zaman na Abuja zai mayar da hankali kan dambarwar siyasar da aka shiga a Nijar bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum da kuma nasarori ko akasi da aka samu kan tattauna samar da matifa.

Wata majiya daga kungiyar ta ce a halin yanzu kasashen na ECOWAS ko kuma CEDEAO ba su da niyar daukar matakin soja a kan Nijar, har ma ta kara da cewa akwai yiwuwar Amurka ta shiga cikin tattauna da sojojin don samar da mafita ta hanyar diflomasiyya.

Sai dai a daya gefen kuma, kasashe Mali da Burkina Faso da tun farko suka nuna goyoyn baya ga juyin mulkin na Nijar, sun aike wata tawaga i zuwa birnin Yamai karkashin Abdoulaye Maïga domin jaddada goyon baya ga al'ummar kasar da suka dandana radadin takunkuman da kugiyoyin ECOWAS UEMOA suka kakaba wa kasar.