EFCC na zargin bankunan Faransa da zama wurin jibge kudaden Nigeria
November 27, 2006Hukumar yaki dayiwa tattalin arzikin Nigeria zagon kasa da rashawa a tace tana sanya fifiko wajen gudanar da binciken bankunan kasar faransa da dama,a harkokin yaki da rashawa da takeyi game da dukiyar kasar.Shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu yace sun gano cewa a wani banki na birnin Paris ne aka jibge wasu makuddan kudade na Nigeria.
A ganawar da yayi da yan jaridan Britania qa birnin London,a makon daya gabata,Malam Ribadu ya zargi kasar faransa da wasu kasashen turai da hada baki da yan Nigeria,domin jibge kudaden kasar da ake sacewa a bankunansu.
A kwanakin baya nedai Nuhu Ribadu ya sanar dacewa da samun yancin Nigeria daga mulkin mallakan Britania shekaru 46 da suka gabata,shugabanin kasar sunyi sama da fadi da kimanin dala billion 384.