1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ensaf Haifar ta Saudiyya ta samu kyautar Sakharov

Gazali Abdou TasawaDecember 16, 2015

An bai wa matar shahararren marubcin taskar blog din nan na kasar Saudiyya Raef Badaoui kyautar 'yancin fadin albarkacin baki ta Sakharov ta Majalisar Turai

https://p.dw.com/p/1HOEU
EP verleiht heute den Sacharow-Pres an Raif Badawi Ensaf Haidar
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Seeger

An bai wa matar shahararren marubcin taskar blog din nan na kasar Saudiyya Raef Badaoui kyautar 'yancin fadin albarkacin baki ta Sakharov ta Majalisar Turai.

An bai wa Ensaf Haifar mai dakin Raef Badaoui wannan kyauta a lokacin wani biki na musamman da aka gudanar a wannan Laraba a birnin Strasbourg.

A jawabin da ya gabatar kafin mika wannan kyauta Shugaban majalisar ta Turai Martin Schulz ya yi kira ga sarki Salmane na Saudiyya da ya yi afuwa ga Raef Badaoui dama sakinsa ba tare da wani sharadi ba.

A karshen shekarar bara ne dai hukumomin Saudiyyar suka yanke wa Raef Badaoui hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekaru 10 da kuma bulala 50 a ko wani mako har a tsawon makonni 20 tare kuma da like taskar sardarwar Blog din nasa a bisa zarginsa da yin kalaman batanci ga addinin Islama.