Erdogan ya amince da rushe majalisar zartarwa
June 9, 2015
Ofishin shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana amincewa da saukar Firaminista Ahmet Davutoglu dan bude fage a kafa sabuwar gwamnati bayan da jam'iyyar shugaban ta rasa rinjaye a majalisa a zaben da aka yi a kasar.
A yanzu abin da ake dako na zama ganin shugaba Erdogan ya ba wa Davutoglu babban aiki na kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Tuni dai jam'iyyun adawa a wannan kasa ta Turkiya suka bayyana cewa zasu nuna turjiya ga duk wani yunkurin shugaba Erdogan na neman kafa gwamnatin hadin gwiwa, abin da ake gani zai iya nakasu ga wannan gwamnati.
Wannan ajiye mukami na Firaminista Davutoglu na zama wata al'ada a siyasar kasar ta Turkiya inda zai ci gaba da zama kan wannan kujerar gwamnati har ya zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati.