1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan: Da hannun Saudiyya a kisan Khashoggi

Zulaiha Abubakar RGB
October 23, 2018

Shugaban kasar Turkiyya ya ce kisan da aka yi wa dan jaridar nan Jamal Khashoggi a Istanbul, an jima da kitsa shi inda ya bayyana wani bangare na sakamakon da suka samu bayan gudanar da bincike.

https://p.dw.com/p/371yi
Erdogan bei AKP-Sitzung im türkischen Parlament
Hoto: picture alliance/AA

Kwanaki kadan da bacewar sanannen dan Jaridar nan Jamal Khashoggi, kasar Turkiyya ta fara gudanar da bincike don sanin dalilin bacewarsa bayan shigar sa karamin ofishin Jakadancin kasar Saudiyya da ke birnin Istanbul. Lamarin da ya tilasatawa gwamnatin kasar Saudiyyan bayyana cewar ya shiga amma ya fita lafiya kafin daga baya ta yi amai ta lashe da cewar Khashoggi ya rasa ransa ne a yayin da kokawa ta kaure tsakanin sa da jami'an tsaro a ofishin jakadancin lokacin da ya ke amsa tambayoyi.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan da ya yi jawabi a zauren majalisar dokokin kasar a wannan Talata, ya daura laifin kisan kan mahukuntan Saudiyya duk da cewa bai ambaci sunan Yarima Muhammad bin Salman wanda Jama'a ke wa kallon kanwa uwar gami a wannan mummunar aika aika ba. Erdogan ya nemi Saudiyya da ta wanke kanta daga zargin hannu a kisan.

Kafin rasuwarsa, Jamal Ahmed Khashoggi marubuci ne a jaridar Washington Post ta Amirka, bayan kasancewarsa mai sukar Yariman kasar Saudiyya Muhammad bin Salman bisa akidunsu na samar da sauye sauye a kasar.

Tun da farko dai makununtan kasar Turkiyya sun bayyana mallakar wani sauti na yadda kisan dan jaridar ya kasance a cikin ofishin jakadancin, ta kuma nemi a mika ma ta wasu mutane goma sha takwas da ake zargi da boye gawar dan Jaridar.