Erdogan ya yi barazanar bude iyakoki
November 25, 2016Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kashedin cewa idan kungiyar tarayyar Turai ta ci gaba matsawa kasar sa, to babu makawa zai bude iyakokin kasar ga dubban 'yan gudun hijira su kwarara zuwa cikin tarayyar Turan. Erdogan ya furta kalaman ne a ranar Juma'ar nan yayin wani jawabi da ya yi wa wani taron mata a birnin Istanbul, kwana daya bayan da majalisar dokokin Turai ta kada kuri'ar jingine tattaunawa da Ankara game da burinta na shiga kungiyar tarayyar Turai.
Yace lokacin da yan gudun hijira dubu 50 suka yi cincirindo a Kapikule da ke iyaka da kasar Girka, kasashen Turai sun yi ta babatu, a sannan suka fara tambayar me zai su yi idan Turkiyya ta bude iyakokinta?, Yana mai cewa idan kungiyar tarayyar Turai ta ci gaba da matsa masa lamba, to kuwa zai bude dukkan iyakokin kasar yan gudun hijira su shiga kasashen Turai.
Ya zargi kungiyar tarayyar Turai da rashin cika alkawuran da ta yi na taimakawa yan gudun hijirar. Kasar Turkiyyar dai ta tsugunar da yan gudun hijirar Siriya fiye da miliyan biyu a cikin kasarta. Jamus ta ce martaba yarjejeniyar da aka cimma alheri ne ga bangarorin biyu