EU na tattaunawa kan rikicin Libiya
January 20, 2020Talla
Guda daga cikin abinda zaman nasu ke mayar da hankali shi ne farfado da sintiri na sojojin kungiyar a Tekun Bahar Rum da nufin tabbatar da cewar an dakile shigar da makamai ga bangarorin da ke rikici da juna.
Ministocin har wa yau za su tabo batun zaman da aka yi kan rikicin na Libiya a jiya a birnin Berlin na nan Jamus, inda ake sa ran za su bada cikakken gyoyon bayansu ga abin da taron ya cimma.
Gabannin kammala wannan zama dai, tuni wasu daga cikin kasashen na EU suka bada goyoyn bayansu ga wannan aiki wanda suke ganin zai taimaka wajen kawo karshen halin dardar da ake ciki a wasu yankuna na gabas ta tsakiya.