EU ta gargadi masu kasuwar bayi a Libiya
November 23, 2017Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana a wannan rana ta Alhamis cewa za ta yi aiki tukuru wajen ganin an samu mafita kan matsalar da 'yan gudun hijira suke ciki a Libiya, inda ita ma ke da ra'ayi na Shugaba Emmanuel Macron da ya nuna bacin ransa kan gudanar da kasuwancin bayi a wannan kasa.
Tun bayan da kafar yada labaran CNN ta fitar da hoton bidiyo kan yadda ake wannan ta'asa ta cinikin bayi da 'yan Afirka bakar fata a hannun Larabawa a Libiya lamarin ya jawo suka tsakanin kasa da kasa. Kwamishinan da ke lura da harkokin 'yan gudun hijira a Kungiyar ta EU Dimitris Avramopoulos ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa tamkar abin da Shugaba Macron ke fadi ne wato sanya mutane a kasuwa babban laifi ne ga dan Adam. Ya ce suna jin abin da ke faruwa a Libiya kan 'yan gudun hijirar kuma ba za a bari ba ya ci gaba da faruwa.