1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na kamari tsakanin Isra'ila da Falasdinawa

Abdoulaye Mamane Amadou ATB
August 6, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kira ga bangarorin da ke rikici da juna su kai zuciya nesa a sabuwar takaddamar da ta barke tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da kungiyar jihad al Islami ta Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/4FDHt
Hayaki ya turnuke Gaza bayan hare haren sojin Israila
Hayaki ya turnuke Gaza bayan hare haren sojin IsrailaHoto: Ismael Mohamad/UPI/IMAGO

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce duk da yake Isra'ila na da hurumin kare kanta daga duk wata barazana, sai dai kuma duk wani matakin da ka iya illata rayuwar fararen hula abin gujewa ne, saboda haka dole ne bangarorin biyu da ke rikici su shafa wa zukatansu ruwan sanyi.

Wannan na zuwa a yayin da ma'aikatar tsaron Isar'ila ta ce a shirye take da ta cigaba da luguden wuta ba sani ba sabo a maboyar 'yan kungiyar Islamic Jihad a zirin Gaza.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Isra'ila ya ce sojojin kasar za su ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza har nan da mako guda, saboda hakan ba wata dama a yanzu ta hawa teburin sulhu don tsagaita wuta.

Isra'ila ta kaddamar da luguden wuta a wasu wuraren da ta kira maboyar 'yan kungiyar Islamic Jihadi a zirin Gaza a ranar Jumma'a, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da wata karamar yarinya 'yar shekaru biyar, baya ga raunata mutane 100, sai dai kungiyar ta Islamic Jihad harba daruruwan rokoki zuwa yankunan Isra'ila a wani mataki na martani.

Tuni dai Masar da ke makwabtaka da yankin ta bayyana anniyar shiga tsakani, da zummar tsagaita wuta da bangarorin ke ci gaba da yi wa juna.