EU ta shiga tsaka mai wuya bayan kammala zabenta
May 27, 2019Talla
Jam'iyyu masu tsananin kishin kasa da masu kyamar baki da kuma masu fafutukar kare muhalli, sun bai wa masu matsakaicin ra'ayi da hadin kan Turai mamaki a zabukan 'yan majalisar dokokin Turan da aka kammala a ranar Lahadi.
Sakamakon farko dai da aka samu a zaben, na cewa a dole masu rajin ganin an sami hadin kan na Turai su nemi kulla sabon kawance.
Sai dai masu matsakaicin ra'ayin da suka hada da European People's Party da gungun 'yan Social Democrats, da za su rasa rinjaye a majlisar mai kujeru 751, na jayayya da kulla kawance da masu tsananin ra'ayin kishin kasa.